TARIHIN HITLER (03)
Bayan Hitler yaga yayi nasara Akan qasashen Turai Sai ya mayar da Akalarsa ga qasar (RUSSIA) rasha Domin yayi mamaya, a shekarar 1941 ne ya qaddamar da mamayar qasar RUSSIA wato Daular Soviet Union mamayar da manyan kwararrin Generals din Shi suka saka ma suna (OPETATION BABAROSSA) wadannan Generals din sun hada da
¶Colonel General Von kliest
¶Colonel General Hoepna Hoth
¶Colonel General Edward Gudarean
Nan take shugaban qasar Russia wato JOSEPH STALIN yayi gaugawar umurni ga sojojin Red Armies wato sojoji rasha da su tunkari Dakarun Germany na Hitler, kwararrin sojojin Nazi na Hitler sun bayyana cewa mamaye rasha bazai wuce wata daya ba kacal, Saidai kash yadda Jamusawa suka zata abun ya canza Domin qasar rasha qasa ce Mai qarfin gaske dukda irin qarfin Sojin Hitler din, Tarihi zai iya bayyana wannan mamayar amatsayin kuskure da Hitler ya tafka.
America, da qawayen ta sun hada rundunar sojoji ta qawance da suke kira (Allies forces) Domin Tunkarar Hitler da qawancen sa na qasa biyu masu qarfi wato ITALY da JAPAN qawancen Mai suna (AXIS power) saboda rinjaye da qasashen America suka samu wannan yasa suka rinjaye sojojin su Hitler inda Sojin rasha suka samu damar raka Dakarun Hitler Har cikin Germany. Wanda a shekarar 1945 shekara biyar ana fafatawa sojojin qawance sun rinjaye rundunar Hitler inda suka shiga Har cikin Germany suka kwace iko da Qasar, masana Tarihi sun tabbatar da cewa ba'a kama Hitler Hannu da Hannu ba wasu ma na cewa ya kashe kansa ne aqarqashin qasa wajen fakewa yayin yaqi (Bunker) .....
Zan cigaba insha ALLAH.
Abbas Ibn Ibrahim Zauma.
Nagaba
ReplyDelete