ƘISSAR SANIYA

 ƘISSAR SANIYA 


✍️ Muhammad Abdulrahman Rano.


Bari kuji wata ƙissa mai ban sha'awa, wadda wani bawan Allah ya shiga wani mugun hali ammar addu'ar mahaifiyarsa ta kuɓutar dashi;


Wannan ƙissar na ciro ta ne daga littafin FALALAR BIN IYAYE DA HAƊARIN SAƁA MUSU, wallafar Sheikh Tijjani Bala ƙalarawi.


Ayoyin ƙissar saniya a cikin Al ƙur'ani ba ɓoyayyiya ba ce, ga kowanne mumini. ko da yake shashinsu ya jahilci rabe-rabenta. To mu, inji mawallafin littafin BIN IYAYE zamu kawota a rarrabe wato filla-filla, domin kwaɗayin kawo misalin da ake iya ji ga yara don su riski ƙololuwar arzikin da zai sauƙo musu idan sun bi iyayensu.


An yi wani mutum mai wadata a zamanin bani Isra'ila, yana da ɗan baffa matalauci. Mawadacin nan ba shi da wani magaji in ba ɗan baffan nan nasa talaka ba. Yayin da ɗan baffan nan yaga mawadacin ya daɗe be mutu ba, sai ya kasheshi don ya gajeshi. Ya ɗauki gawar ya kai wani ƙauye ya jefata a filinsu. Sai ya dawo yana neman sakamakon kashe wannan mai kuɗin a kan wasu. Sai ya kawo ƙarar wasu mutane gaban Annabi Musa yana da'awar su ne suka kashe mai kuɗin nan (wato ba shi bane).


Annabi Musa ya tambayi mutanen nan ko su ne suka kashe wannan mai kuɗin? Sai mutanen nan suka musa suka ce ba sune suka kashe shi ba. Sai Annabi Musa ya kasa gane lamarin wanda aka kashe ɗin. Sai mutanan da aka ƙallafawa kisan mai kuɗin suka roƙi Annabi Musa akan ya roƙi Allah don ya tona asirin wanda ya kashe mai kuɗin nan.


Sai Annabi Musa ya umarcesu da su yanka Saniya. Inda yace; "Haƙiƙa Allah yana umartaku ku yanka Saniya". Sai su ka ce yanzu ka dinga yi mana izgili? Ta yaya muna roƙon ka akan lamarin wanda aka kashe don mu san mai kisan, kai kuma kana uamrtarmu da yanka saniya? Sun faɗi hakane don ganin nisan abinda ke tsakanin al'amarin biya a zahiri. Wato sanin wanda ya kashe me dukiya da kuma yanka Saniya.




Sai Annabi Musa yace "Ina neman tsari in zama daga cikin jahilai, in zama daga cikin masu yiwa Muminai izgili". Da Mutanen suka san yanka saniyar wani nufi ne daga Allah Azza-wa jalla, sai suka nemi a siffanta musu irin saniyar da zasu yanka. In da sun dogara da yanka kowacce irin saniya da ta isar musu, amma Ina? Sai suka matsawa kansu Allah kuma ya matsa musu, wadda akwai hikima akan hakan.


Akwai wani Mutum nagari a cikin Bani Isra'ila, yana da ɗa kuma yana da ƴar maraƙa, ta ɗaukar kaya. Sai ya ɗauki wannan ƴar maraƙa ya kai ta wata sarƙaƙiya a jeji, ya ce ya ubangiji na ba ka ajiyar wannan maraƙa ta ɗana har sai ya girma. Sai Allah yayi wa mutumin rasuwa, ƴar maraƙa kuwa tana jeji cikin sarƙaƙiya. Ita ba babba ba ba ƙarama ba, kowa ta gani sai ta fita a guje.


Da ɗan mutumin nan ya girma sai ya zama mai biyayya ga mahaifiyarsa, ya zama yana kasa dare gida uku, yana sallah a kashi ɗaya, yana bacci a kashi ɗaya, kashi ɗaya kuma yana zama a kusa da mahifiyarsa. Idan gari ya waye kuma se ya tafi yayo itace ya ɗauko a gadan bayansa ya kawo kasuwa ya sayar da shi yadda ya so, ya kasa kuɗin itacen kashi uku; yayi sadaka da kashi ɗaya, yaci kashi ɗaya, ya bawa mahaifiyarsa kashi ɗaya.


A wata rana sai ta ce da shi mahaifinka ya bar maka gadon maraƙa, ya ba wa Allah ajiyarta a jeji kaza. Ka je ka roƙi ubangijin Ibrahim da Ismail da Ishaƙ da Ya'akub ya dawo maka da maraƙarka. Alamar da zaka gane ta idan ka dubeta zaka zaci hasken ruwa ne yake fitowa daga fatarta, ana kiran maraƙar da sunan zinariya saboda kyanta da fatsi-fatsinta.


Sai yaron ya je jejin ya kuwa ganta tana kiwo. Sai ya ƙwalla mata kira ya ce, ina yi miki magiya don Ubangijin Isma'il da Ishak da Yakubu ki zo. Sai ta taho tana tafiya da ƙafarta har ta tsaya gaban yaron nan. Sai ya kama wuyanta ya na janta, sai ta yi magana da yardar Allah ta ce, ya kai wannan saurayi mai biyayya ga mahaifiyarsa, ka hau kaina ya fi sauƙi gareni.


Sai yaron yace mahaifiyata ba ta ce in hauki ba, cewa ta yi in kama wuyanki. Sai saniyar ta ce, Na rantse da Ubangijin Bani Isra'ila da ka hauni da bazaka iya iko da ni ba har abada, amma yanzu ka tafi, idan da za ka ce da dutse ya tunɓuko tun daga tushensa ya taho ta re da kai da se ya yi, saboda biyayyarka ga mahaifiyarka. Sai saurayin ya taho da maraƙar zuwa mahaifiyarsa, uwar ta ce da shi, kai talaka ne, baka da dukiya yin itace da rana da tsayuwar dare da kake yi yana wahalar da kai, ka tafi ka siyar da wannan saniya.


Ya ce nawa zan sayar da ita? Ta ce dinare uku. kadda ka siyar da ita va tare da shawarata ba, kuɗin saniyar dinare uku ne. Sai ya tafi da ita kasuwa sai Allah ya aiko mala'ika dan ya gwada halittarsa, ga ikonsa don ya jarrabi saurayin da biyayyarsa ga mahaifiyarsa; Allah masani ne da shi. Sai  Mala'ikan ya ce da shi, nawa za ka sayar da wannan saniyar? Sai saurayin yace dinare uku zan sayar da ita, amma da sharaɗi sai uwa ta ta yarda.


Sai Mala'ikan ya ce ni na siya dinare shida amma kada ka shawarci mahaifiyarka. sai saurayin ya ce da zaka bani dinare nauyin saniyar da bazan karɓa ba sai da yardar mahaifiyata. Sai ya koma da ita wajen mahaifiyarsa ya bata labarin an siya dinare shida. Sai ta ce dashi koma da ita ka siyar dinare shida a bisa yarda ta.


Sai ya sake komawa da ita kasuwa sai Mala'ikan yazo yace ka nemi yardar mahaifiyarka? Ya ce I, sai de ta umarceni kada in rage wani abu daga dinare shida, sai na nemi umarninta. Sai Mala'ikan yace to ni zan baka dinare goma sha biyu, amma a bisa sharaɗi ba se ka nemi umarninta ba. Sai saurayin yaƙi yarda ya koma da maraƙar wajen mahaifiyarsa ya bata labarin yadda sukayi da Mala'ikan.


Sai ta ce ai wanda yake zuwa yake taya maraƙar nan, Mala'ika ne (a surar ɗan Adam) don ya jarraba ka. Idan yazo maka kace dashi, shin zaka uamrce mu mu sayar da wannan saniya ko kuwa? Sai saurayin ya gayawa Mala'ikan hakan, sai Mala'ikan yace dashi, tafi wajen mahaifiyarka ka ce da ita, ki riƙe wannan saniya.


Haƙiƙa Annabi Musa ɗan Imrana shi ne zai saye ta daga wajenku, saboda wani mutum da aka kashe shi A cikin Bani Isra'ila. Kada dai ku sayar da ita sai da dinarai a cike a cikin fatarta. Ku riƙe ta, Allah Ta'ala ya ƙaddara wa Bani Isra'ila yanka wannan Saniya.


Ba su gushe ba suna siffanta Saniya iri-iri har aka siffanta musu wannan saniya, (Su Bani Isra'ila kenan) don sakamako ga wannan saurayi akan biyayyarsa ga mahaifiyarsa, saboda falala da rahama ga Allah. Sannan Allah Ta'ala ya umarci mutanensa da cewa su daki mataccen nan da wani ɓangare na jikin saniyar nan. da sukayi haka sai mataccen nan ya tashi da yardar Allah ta'ala.


Jini yana kwaranya daga wuyansa yana cewa wane ne ya kashe ni, wato ɗan baffansa; sannan ya faɗi matacce nan take a wurin. sai aka hana wanda ya kashe shi, ya gajeshi. kayi duba ya kai mai karatu acikin wannan ƙissar zakaga sakamakon biyayyar iyaye da kuma sakamakon mummuna aiki tunda a ƙarshe be samu dukiyar da yayi kisan ɗan ita ba.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

TARIHIN HITLER (06)

Dangane da Schorlarship ɗin gwamnatin jihar Kano