Dangane da Schorlarship ɗin gwamnatin jihar Kano

  

A safiyar yau, 16/05/23 Gwamnatin Kano ta fitar da sanarwar fara scholarship zuwa ƙasashen ƙetare na ɗalibai masu First Class. Idan ba'a manta ba,  wannan yana daga alqawarurrukan da gwamnatin ta ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe. 



SHARUƊAN DA AKE BUKATA MAI NEMA YA CIKA SUNE:

—Ya kasance mai nema cikakken ɗan jihar Kano ne

—Ya kasance ya gama digiri da First Class a jami'ar da take shaidar tantancewa a hukumance. 

—Ya kasance mai ƙoshin lafiya


ABUBUWAN DA AKE BUƘATA SUN HADA DA: 

—Shaidar zama ɗan jihar Kano

—Takardar haihuwa

—Shaidar gama makarantar firamare

—Shaidar kammala jarabawar sakandare (WASC/GCE/SSCE) 

—Shaidar gama digiri mai ɗauke da First Class. 

—Transcript da makamantansu


Za'a kai waɗannan takardu ne sakatariyar tantancewa dake tsohon dakin taro na ofishin sakataren Gwamnatin Kano kan titin Wudil Road. 


A kula: KADA A WUCE SATI 2 BAA KAI WADANNAN TAKARDU BA. 


Akwai website da mai nema zai shiga ya cike bayanan sa wato;

 👇👇

Scholarship link



A saurari ƙarin bayani na gaba.


Daga: ✍️

Aminu Rabiu Tela

Mai wayar da kai (na sa kai) akan harkokin tallafin karatu na gwamnatin Kano.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

TARIHIN HITLER (06)