TARIHIN HITLER (09)

 IYALAN HITLER. 



Saboda Aikin soja Hitler ya Dade Bai yi Aure ba Domin aloqacin Hankalin Shi Baya ta wannan,  Saidai Bayan zaman sa shugaban Germany loqacin ya samu cikakken iko ya Aure wata Yarinya, Sun so suyi amfani da ita Domin a kashe Hitler amma Ina tana matuqar son Hitler, Domin loqacin da aka Ci Sojojin Hitler da yaqi wasu masu kawo Tarihi sun bayyana cewa Shi da matar sa sun kashe kansu ne an Tarar da gawar su tare. 


Saidai 

Kuma loqacin yaqin Duniya na farko (WWI) loqacin Yana qaramin soja Bayan sojojin Germany sun shiga Yankin faransa a inda aka jibge su akwai wani qauye Wanda awannan qauyen Adolf Hitler ya sabu da wata Mata Bafaransiya, Kuma Har ya Aure ta  Aure irin nasu, Saidai Kuma wannan qasar ba tashi bace yaqi ya kawo su Bayan wani loqaci Bayan an Gama yaqi Hitler yabar qasar ba tare da wannan matar ba, Domin yasan ana iya kashe Shi Idan ya shigo da wannan matar cikin qasar Germany amatsayin ta na "yar faransa Shi Kuma amatsayin sa na qaramin soja awancan loqacin yaqin Duniya na farko. Ashe ashe wannan matar tasa tana dauke da Cikin dansa Bai Sani ba. Ana ahaka tsakanin yaqin Duniya na farko Dana biyu shekaru 



25 ne 1914 - 1939 kenan wannan matar Yaron ta ya Girma Har ya shekara 24, Hitler Bai san da Dan sa ba, amma ita wannan matar ko da ake rikici da Hitler tasan komi amma ita da Danta Dan Hitler suna cikin qasar faransa ne.


Wannan Yaron Kuma akayi wani rashin sa'a ya shiga Aikin soja cikin sojojin faransa ita Kuma France tana Fada da Germany ne aloqacin da yaqin Duniya na biyu ya barke iko Sai ALLAH 😀 Yaro Yana fada da ubansa kenan amma Yaron Yana cikin rashin Sani, amma uwar Shi tasan da haka. Yaro ALLAH yayi mashi tsawon rai awannan yaqin ba'a kashe Shi ba Har aka Gama, loqacin da uwar wannan Yaron tsohuwar matar Hitler zata mutu Sai ta bayyana masa wasu kalmomi masu ban tsoro tace masa " The Unknown German soldier in world War One I is your father"  ma'ana  Sojan nan da baiyi wani suna ba amma ga yaqin Duniya na farko shine baban ka " kenan abun ya fito fili saboda loqacin Hitler ba'a san Shi ba qaramin soja ne, Kai daga Qarshe ta bayyana masa lallai Adolf Hitler shine uban Shi, Hankalin yaro ya tashi Hukumomin France suka shiga cikin lamarin aka cigaba da bincike akayi Awon Jini DNA din su da Hitler yazo daya, malaman Genetics suka tabbatar shakka babu wannan Yaron Dan Hitler ne. Amma ba'a kashe Shi ba Domin ma Har yabar Aikin soja ya Koma aiki jirgin qasa! Mutane sun ta tsangwamar wannan mutumin Saidai Mai Gama ta gama Domin yayi Aure shima Yana da "ya" ya  ataqaice zuriyar Hitler akwai burbushin ta Har ayanzu. Saidai an juje kwakwalwar su basu alfahari da Hitler da Aikin sa.


Abbas Ibrahim Zauma

(mu haɗu a rubutu na ƙarshe!).

Comments

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa É—alibai bashin karatu a Najeriya

TARIHIN HITLER (06)

Dangane da Schorlarship É—in gwamnatin jihar Kano