TARIHIN HITLER
Marubucin wannan tarihi shine; Abbas Ibrahim Zauma.
TARIHI
WAYE ADOLF HITLER?
Adolf Hitler haifaffen Dan qasar (AUSTRIA) Mu kula akwai babanci tsakanin qasar AUSTRIA da AUSTRALIA. Qasar AUSTRIA wata qaramar qasa ce dake makwaftaka da Qasar GERMANY dake turai. An haife Adolf Hitler a shekarar "1889" Adolf Hitler tun Yana qarami ya rasa iyayen sa yayi rayuwar maraici Kuma yasha wahalar rayuwa, Hitler mutum ne Mai baiwar Zane-zane (Arts) Kuma mutum ne Mai son Tarihi, ya taso Kuma ya Girma acikin qasar sa ta haihuwa AUSTRIA Mai makwaftaka da GERMANY, mutun ne Mai Qin Jinin Yahudawa Kuma Yan tuhumar shugabannin Turai da Daure ma yahudawa suna juya turai da qasashen su na Gado yadda suke so! Tare da zargin shugabanni da fifita yahudawa Akan "Yan Asalin qasashen su, loqacin da wannan ra'ayin ya fara bayyana ga wannan matashin mutun Sai aka daqile yunkurin sa na shiga Aikin soja Kuma aka rufe Shi a gidan yari tsawon loqaci, Bayan fitowar sa Sai ya wallafa wani littafi Mai suna (MY STRUGGLE} Ma'ana GWAGWARMAYA TA.
Daga nan Bayan rashin samun cikakkiyar dama daga Qasar sa ta AUSTRIA Sai ya yanke shawarar yaga Indigent nashi na qasar ya Koma qasar GERMANY Mai makwaftaka da AUSTRIA Wanda Hitler yayi imanin cewa qasar Germany ma qasar su ce ta Gado Domin ma kusan Harshen su daya Kuma Al'adun su daya Qasar Germany ta karbi baquncin matashi Hitler ya zama Dan qasa ya samu sabon (NATIONALITY) Wanda yayi Hakane a shekarar 1913 ana saura shekara daya a fara Gwabza yaqin DUNIYA na farko (WWI} nan take Hitler ya shiga Aikin soja Amma cikin Volunteer ma'ana Sojan Sakai.
Ashekarar 1914 yaqin Duniya na farko ya barke tsakanin qasashen turai inda qasar Germany ke goyon Bayan qasar Servia wacce aka kashe ma yarima (Franz Ferdinand). Dakarun Germany sun yaba ma ma kokarin Hitler ganin cewa Bai ma samu horo irin na Sojan Jamus cikakke ba Amma yayi hubbasa ga yaqin, wannan yasa yayi farin Jini gidan soja Har aka bashi muqami, Bayan kammala yaqin Duniya na biyu Sannu a hankali Hitler na qara karbuwa a Germany kafin ya bayyana cikakkiyar adawa da yahudawa Sai ya kafa Qungiyar siyasa Mai suna (NAZI CONGRESS) Ya karbu a gidan siyasa inda a shekarar 1933 Hitler ya Ci zabe amatsayin shugaban qasar Germany bisa tsarin (CHANCELLOR) Kuma shugaban Hafsan sojin Germany Mai cikakken iko. Aloqacin ne wajen jawabin sa na farko a Garin (NEMERINBERG) yake bayyana haramta MA Mata karatu a matakin Jami'ia Kuma ya karbe ikon manyan ofisosa da Mata ke jagoranta, daga nan alaqar sa da qasashen Turai Kamar France, England Tayi tsami qungiyoyin waje suka tayar da Mata suna zanga zanga cikin Germany Domin nuna adawa da Tsatstsauran ra'ayin Hitler Akan Mata da Kuma yahudawa, ganin haka fa Hitler Bai yi qasa a Guiwa ba ya shiga kisan yahudawa Sai da ya kashe bayahude miliyan shida (Six millions Jews) inda ya ayyana su amatsayin Bala'i ga qasar sa da Kuma Duniya, tsarin da yabi wajen kisan su Shi suke kira da suna (HOLOCAUSTS) ya Sanya a makarantu koyar da Dalibai Qin yahudawa. kuma doka ce ko Ruwa aka kama ka kaba bayahude kashe ka za'ayi kaida Shi, Domin haka ya karanta Tarihi a shekarun da Suka shude qasar Germany ta taba korar yahudawa acikin qasar.
Hitler ya hada Kai da Qasar ITALY da Qasar JAPAN sun qulla kawance inda Ashekarar 1939 Hitler yayi umurni ga Generals din Shi dasu kwace ikon qasar POLAND, Bayan nan Hitler ya tura gagarumar Runduna su kwace qasar FRANCE , SPAIN, PORTUGAL duka qasashen turai da basu Goya masa Baya Sai ya mamaye su da karfin soji, wannan Abu ya tayar ma da Qasar England wacce ke a gefen Germany amma Ruwan teku sun shiga tsakanin su Wanda haka yasa ita ma England din Bai mamaye ta ba. Amma sojojin Sama sunyi luguden wuta acikin biranen qasar England, lamarin Hitler ya tayar da Hankalin hatta America dukda cewa America Hankalin ta ya karkata ne ga qasar JAPAN da fadan gasar Tattalin Arziki ya rikide zuwa wuta-wuta, amma Nan take shugaban qasar England wato Prime Minister na loqacin da suke kira (WINSTON CHURCHILL) Ya aika da saqon Gaugawa ga shugaban America (FRANKLIN DELANO ROSOVELT)
Kan cewa Hitler na barazana ga hatta qasar England data rage Mai motsi a loqacin, yayi Kiran karfafa qawancen soja Domin taka ma Germany Birki, ita Kuma America yaqin ta da Dan Hakin daka raina wato JAPAN ya Sha Mata Kai amma a haka ta cije ta Aika ta rudunar sojoji qasar England Domin Tsaurara Tsaro!
Baban Hiter Kenan
Hitler yana ɗan shekara goma sha uku (13).
Mahaifiyar Hitler.
Hitler Bayan ya girma 👆
Duk nan dakarun Hitler ne 👆
sojojin Nigeria lokacin da America tayo hayarsu. k👆😂😂
SHIN MEYASA HITLER YA MAMAYI RUSSIA 1941.?
Yahudawa lokacin da Hitler ya kamasu, in kun lura sun rame 👆
Hitler ya Tuhumci qasar Rasha (Russia) Da bin muradun Yahudawa tare da goyon Bayan England da America ga siyasar Duniya Kuma Hitler ya tayar da tsohuwar gaba ta yaqin Duniya na farko inda sojojin Jamus suka Sha Kashi ga hannun rashar wannan yasa Hitler yaga cewa yanzu ya samu damar dauko waccan fansar, Saidai kash aloqacin JOSEPH STALIN shugaban rasha ya kira Zaman Sulhu tsakanin Shi da Hitler amma Ina yayi wannan Kiran ne mamayar na qasa ga Sati daya Kamar yadda Dan leqen asirin rasha Mai suna (Garhard Kegel) Ya hakaito. Wannan mamayar Tayi sanadiyar rushewar Gwamnatin Nazi ta Hitler.
BARAZANAR KISA DA AKAYI MA HITLER.
Tabbas Hitler ya fuskanci barazanar kisa abunda ake kira (Assasination) A Tarihi shine mutun mafi tsallake ma hare-hare ba tare da anyi nasara Akan Shi ba, qasashen England, America sun yi ta amfani da Baragurbi cikin qasar Germany Wanda acikin sojojin Hitler manyan Generals din sa an samu dayawa da yunqurin kashe Hitler aloqacin,
Adolf Hitler ya tsallake Hari Mai muni daya Bayan daya Har Hari 40 Arba'in.
Akwai loqacin da suna cikin Tattaunawa kawai aka jefo qaramin Bomb na Hannu wato (Hand Grenade) Bomb din ya tashi amma Hitler ya tsira a qarqashin Teburin Tattaunawa, inda wadanda yake Tattaunawa dasu duka suka mutu! Wanda duk loqacin da akayi yunqurin kisan Hitler jami'an sa na sirri (SS) zasuyi bincike su Gano wadanda suka kitsa sharrin, Idan ya kama Sojan sa da laifi Bindiga ake ba Sojan ya harbi kanshi, ko Kuma asaka mashi rigar Bomb ta tashi dashi, akalla a Qididdigar da akayi Saidai ya kashe Generals din Shi fiye da 80 Tamanin, bisa laifuffukan rashin Da'a da Kuma yunqurin kashe Shi.
Adolf Hitler Bai nemi qulla qawance da Qasar Italy ba Saidai ita Italy ita ta nemi su hada Kai, Wanda a Shekarar 1939 Shugaban qasar ITALY Mai suna BENITO MUSSOLINI Yakai ziyarar ban Girma ga Adolf Hitler Har cikin Germany, inda yaje sanye da Kayan sojoji Shi wannan mutumin fahimtar su tazo daya da Adolf Hitler Kuma manufar su ta zama iri daya Domin shima baida wasa shiyasa su yahudawan a yanzu suka saka shugaban na Italy wato (Benito Mussolini) Cikin list na miyagun mutane masu mulkin kama karya a Tarihi wato mulkin (FACISM) na DICTATORSHIP. Tabbas aloqacin yahudawan Italy sun Gamu da Bala'i Domin Yana daga cikin yarjejeniyar da Suka qulla na cewa Ya halakar da Yahudawan
qasar sa. Kuma ya Amince da haka.
IYALAN HITLER.
Saboda Aikin soja Hitler ya Dade Bai yi Aure ba Domin aloqacin Hankalin Shi Baya ta wannan, Saidai Bayan zaman sa shugaban Germany loqacin ya samu cikakken iko ya Aure wata Yarinya, Sun so suyi amfani da ita Domin a kashe Hitler amma Ina tana matuqar son Hitler, Domin loqacin da aka Ci Sojojin Hitler da yaqi wasu masu kawo Tarihi sun bayyana cewa Shi da matar sa sun kashe kansu ne an Tarar da gawar su tare.
Saidai
Kuma loqacin yaqin Duniya na farko (WWI) loqacin Yana qaramin soja Bayan sojojin Germany sun shiga Yankin faransa a inda aka jibge su akwai wani qauye Wanda awannan qauyen Adolf Hitler ya sabu da wata Mata Bafaransiya, Kuma Har ya Aure ta Aure irin nasu, Saidai Kuma wannan qasar ba tashi bace yaqi ya kawo su Bayan wani loqaci Bayan an Gama yaqi Hitler yabar qasar ba tare da wannan matar ba, Domin yasan ana iya kashe Shi Idan ya shigo da wannan matar cikin qasar Germany amatsayin ta na "yar faransa Shi Kuma amatsayin sa na qaramin soja awancan loqacin yaqin Duniya na farko. Ashe ashe wannan matar tasa tana dauke da Cikin dansa Bai Sani ba. Ana ahaka tsakanin yaqin Duniya na farko Dana biyu shekaru
25 ne 1914 - 1939 kenan wannan matar Yaron ta ya Girma Har ya shekara 24, Hitler Bai san da Dan sa ba, amma ita wannan matar ko da ake rikici da Hitler tasan komi amma ita da Danta Dan Hitler suna cikin qasar faransa ne.
Wannan Yaron Kuma akayi wani rashin sa'a ya shiga Aikin soja cikin sojojin faransa ita Kuma France tana Fada da Germany ne aloqacin da yaqin Duniya na biyu ya barke iko Sai ALLAH 😀 Yaro Yana fada da ubansa kenan amma Yaron Yana cikin rashin Sani, amma uwar Shi tasan da haka. Yaro ALLAH yayi mashi tsawon rai awannan yaqin ba'a kashe Shi ba Har aka Gama, loqacin da uwar wannan Yaron tsohuwar matar Hitler zata mutu Sai ta bayyana masa wasu kalmomi masu ban tsoro tace masa " The Unknown German soldier in world War One I is your father" ma'ana Sojan nan da baiyi wani suna ba amma ga yaqin Duniya na farko shine baban ka " kenan abun ya fito fili saboda loqacin Hitler ba'a san Shi ba qaramin soja ne, Kai daga Qarshe ta bayyana masa lallai Adolf Hitler shine uban Shi, Hankalin yaro ya tashi Hukumomin France suka shiga cikin lamarin aka cigaba da bincike akayi Awon Jini DNA din su da Hitler yazo daya, malaman Genetics suka tabbatar shakka babu wannan Yaron Dan Hitler ne. Amma ba'a kashe Shi ba Domin ma Har yabar Aikin soja ya Koma aiki jirgin qasa! Mutane sun ta tsangwamar wannan mutumin Saidai Mai Gama ta gama Domin yayi Aure shima Yana da "ya" ya ataqaice zuriyar Hitler akwai burbushin ta Har ayanzu. Saidai an juje kwakwalwar su basu alfahari da Hitler da Aikin sa.
ALHAMDULILLAH DA WANNAN NE TAƘAITACCEN TARIHIN HITLER YA KAMAMALA MUNA FATAN KUNJI DAƊIN WANNANAN TARIHI KUMA KUN SAMU DARASI DA DAMA A CIKINSA.
KU KASANCE DANI
👇
DOMIN SAMUN TARIHI DABAN-DABAN DA KUMA RUBUTUTTUKA WANDA ZASU AMFANEKU A RAYUWAR DUNIYA DA LAHIRA.
Nagode!
Comments
Post a Comment