TARIHIN HITLER (08)

 BARAZANAR KISA DA AKAYI MA HITLER. 


Tabbas Hitler ya fuskanci barazanar kisa abunda ake kira (Assasination) A Tarihi shine mutun mafi tsallake ma hare-hare ba tare da anyi nasara Akan Shi ba, qasashen England, America sun yi ta amfani da Baragurbi cikin qasar Germany Wanda acikin sojojin Hitler manyan Generals din sa an samu dayawa da yunqurin kashe Hitler aloqacin, 

Adolf Hitler ya tsallake Hari Mai muni daya Bayan daya Har Hari 40 Arba'in. 



Akwai loqacin da suna cikin Tattaunawa kawai aka jefo qaramin Bomb na Hannu wato (Hand Grenade)  Bomb din ya tashi amma Hitler ya tsira a qarqashin Teburin Tattaunawa, inda wadanda yake Tattaunawa dasu duka suka mutu! Wanda duk loqacin da akayi yunqurin kisan Hitler jami'an sa na sirri (SS) zasuyi bincike su Gano wadanda suka kitsa sharrin, Idan ya kama Sojan sa da laifi Bindiga ake ba Sojan ya harbi kanshi, ko Kuma asaka mashi rigar Bomb ta tashi dashi, akalla a Qididdigar da akayi Saidai ya kashe Generals din Shi fiye da 80 Tamanin, bisa laifuffukan rashin Da'a da Kuma yunqurin kashe Shi. 



Adolf Hitler Bai nemi qulla qawance da Qasar Italy ba Saidai ita Italy ita ta nemi su hada Kai, Wanda a Shekarar 1939 Shugaban qasar ITALY Mai suna BENITO MUSSOLINI Yakai ziyarar ban Girma ga Adolf Hitler Har cikin Germany, inda yaje sanye da Kayan sojoji Shi wannan mutumin fahimtar su tazo daya da Adolf Hitler Kuma manufar su ta zama iri daya Domin shima baida wasa shiyasa su yahudawan a yanzu suka saka shugaban na Italy wato (Benito Mussolini) Cikin list na miyagun mutane masu mulkin kama karya a Tarihi wato mulkin (FACISM) na DICTATORSHIP. Tabbas aloqacin yahudawan Italy sun Gamu da Bala'i Domin Yana daga cikin yarjejeniyar da Suka qulla na cewa Ya halakar da Yahudawan 

qasar sa. Kuma ya Amince da haka. 


Abbas Ibrahim Zauma

(mu haɗu a rubutu na tara).

Comments

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

TARIHIN HITLER (06)

Dangane da Schorlarship ɗin gwamnatin jihar Kano