HAƊARIN DA KE CIKIN KAƊAITAR NAMIJI DA MACE
Daga: Malam Ɗayyabu Umar Memai Rano.
Itade kaɗaita da ƴa mace se kai se ita wacce ba matarka ba kuma akwai aure tsakaninku da ita abune me hadari a addinin musulunci. wannan ce tasa fiyayyen me ƙaunarmu ɗan gata Allah wanda ba'a taɓa kamarsa ba kuma baza'ayiba Annabi Muhammad (ﷺ) yace: "kadda wani mutum ya kaɗaita da mace se tare da muharraminta, wato wanda babu aure a tsakaninsu" Imamul Muslim ne da Bukari suka rawaito Hadisin. wanda aka karɓoshi daga Abdullahi ɗan Abbas (Radiyallahu Anhuma).
Wajibine mubi umarni na Annabi (ﷺ) kadda mace da namiji su keɓe a yanayin zance na zawarawanmu ko ƴan matanmu da ke gidajenmu ko duk wata mu'amala da tasa se namiji da mace sun haɗu don kaucewa afkuwar zina. Mu Sani dukkan zinar da take faruwa idan kabi a hankali zakaga bata faruwa se da Namiji da mace suka keɓe a inda babu me ganinsu.
✍️ Muhammad Abdulrahman Rano
09 Jumada Sani 1444 AH
02 January 2023 M
Comments
Post a Comment