DALILIN DA YASA DUK ME HANKALI BAZE DENA SALLAR NAFILA BA.
Daga; Mal. Dayyabu Umar Memai Rano.
A Hadisin da aka karbo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) wanda Abu Dawud ya rawaito, Annabi (ﷺ) yace; "farkon abinda za'a yiwa mamaci hisabi dashi a ranar alkiyamah a ayyukansa shine Sallah, Allah ze cewa mala'iku {Alhalin ya sani} “ku duba sallar bawana ya cikata ko ya tauyeta? Idan ta kasance cikakkiya se a rubuta cikakkiya a gareshi, idan wani abu ya tawaya sai Allah yace ku duba ko bawana yanada sallar nafila, idan yanada sallar nafila se Allah yace ku cikawa bawan sallolinsa na farilla da sallarsa ta nafila”sannan a karbi sallolin".
Mu sani ana karba fa Aljannah zaka tafi, kuma da temakon sallarka ta nafila. Idan hakane me hankali baze yarda ya dinga wasa da sallolin nafila ba.
Rubutawa ✍:
Muhammad Abdulrahman Rano
Comments
Post a Comment