TARIHIN HITLER (05)

Hitler Sunan baban Shi kenan Shi Kuma (ADOLF) yake. 


(Hitler Alois  Schicklgruber) wannan shine baban (Adolf)  Shi Kuma Hitler Alois baban Shi shine (Schicklgruber) Shi Kuma baban Shi shine ( Johann Georgiedler)  

Anan mun ambaci kakan (Adolf Hitler) na biyu bangaren Uba,  Baban (Adolf Hitler)  Ya Auri uwar Hitler Mai suna (klara Polz)  Kuma wannan matar itace matar sa ta biyu da Aure Bayan rabuwar sa da ita ya auro uwar (Adolf Hitler) an Auri mamar sa ne a shekarar "1885" 

Baban Adolf kenan wato (Hitler) 
Alois Schicklgruber 👆


(Adolf Hitler) Yana da yayye amma wadanda ba uwar su daya ba ma'ana diyan tsohuwar matar baban Shi Kamar babbar diyar sa (Angela) 


Ashekarar 1886 uwar (Adolf Hitler) ta haife yaro Mai suna (Otto) Amma ya mutu, ta sake haifar wani (Gustov.) shima ya mutu,   shekarar 1889 Ta haifi (Adolf Hitler) Wanda shine danta na uku 3 , Ashekarar 1896 ta haifi Qanwa ga Adolf Hitler Sunan ta (Paula Hitler) Talauci da quncin rayuwa ya saka baban sa rashin zama wuri daya Wanda Har Aikin (shoemaker) saida yayi kafin ya samu wani qaramin Aikin Gwamnati, (Adolf Hitler) Ya fara tasowa amma kuma baban sa ya tsufa ya mutu Yana da shekara 58 aloqacin (Adolf Hitler) Yana yaro qarami Dan shekara (13) a shekarar 1903.


Adolf Hitler lokacin yana É—an shekara (13).

 wannan mutuwar ta baban sa ta qara saka rayuwar sa cikin kunci inda Har wannan yayi sanadiyar watsewar sauran "Yan uwan Shi na haihuwa dashi daga Garin ( Döllersheim) wani qaramin kauye cikin qasar ta Austria, Bayan mutuwar baban sa da shekara shida uwar (Adolf Hitler) wato Klara Polz itama ta mutu a shekarar 1907  Hitler ya zama maraya. Acikin


 

Mahaifiyar Adolf Hitler kenan (Klara polz) 👆

" Yan uwan Shi (Paula Hitler) wato Qanwar sa ita ta rayu , Hitler ya kasance baida wani Dan uwa da suke uwa daya Sai Qanwar sa qarama, Ya taso cikin qasar wahalce, Yana da fasahar Zane Zane Kuma yakasance Yana Qin Jinin yahudawa arayuwar Shi. 


SHIN KO MIYE DALILIN SA NA QIN YAHUDAWA? 


Abunda muka iya ganowa na Tarihi Kan kiyayyar da Hitler yake yi ma yahudawa Yana daga Dalilin Barkewar Cutar (BURVONIC PLAGUE)  Wata Cuta ce Epidemic data taba bayyana shekaru Dadadewa a nahiyar turai a qarni na (13th)  Wanda a shekarar 1353 acikin turai cutar ta bayyana akalla mutun miliyan ashirin da biyar suka mutu (25 million people) Kuma a qarni na (14th) ta sake bayyana inda wannan ya harzuqa Turawa suka shiga bincike Sai suka Gano ashe Yahudawa su suka qirqiro da wannan cutar, wannan yasa aka riqa korar su daga turai aka kama su ana qona su da ransu, wannan zanen hoton Tarihi ne loqacin da ake qona yahudawa Bayan an Gano su suka qirqiro da cutar.




Mu haÉ—u a rubutu na shida.

✍️ Abbas Ibrahim Zauma

Comments

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa É—alibai bashin karatu a Najeriya

TARIHIN HITLER (06)

Dangane da Schorlarship É—in gwamnatin jihar Kano