TARIHIN HITLER (02)

A shekarar 1914 yaqin Duniya na farko ya barke tsakanin qasashen turai inda qasar Germany ke goyon Bayan qasar Servia wacce aka kashe ma yarima (Franz Ferdinand). Dakarun Germany sun yaba ma ma kokarin Hitler ganin cewa Bai ma samu horo irin na Sojan Jamus cikakke ba Amma yayi hubbasa ga yaqin, wannan yasa yayi farin Jini gidan soja Har aka bashi muqami, Bayan kammala yaqin Duniya na biyu Sannu a hankali Hitler na qara karbuwa a Germany kafin ya bayyana cikakkiyar adawa da yahudawa Sai ya kafa Qungiyar siyasa Mai suna (NAZI CONGRESS) Ya karbu a gidan siyasa inda a shekarar 1933 Hitler ya Ci zabe amatsayin shugaban qasar Germany bisa tsarin (CHANCELLOR) Kuma shugaban Hafsan sojin Germany Mai cikakken iko. Aloqacin ne wajen jawabin sa na farko a Garin (NEMERINBERG) yake bayyana haramta MA Mata karatu a matakin Jami'ia Kuma ya karbe ikon manyan ofisosa da Mata ke jagoranta, daga nan alaqar sa da qasashen Turai Kamar France, England Tayi tsami qungiyoyin waje suka tayar da Mata suna zanga zanga cikin Germany Domin nuna adawa da Tsatstsauran ra'ayin Hitler Akan Mata da Kuma yahudawa, ganin haka fa Hitler Bai yi qasa a Guiwa ba ya shiga kisan yahudawa Sai da ya kashe bayahude miliyan shida (Six millions Jews) inda ya ayyana su amatsayin Bala'i ga qasar sa da Kuma Duniya, tsarin da yabi wajen kisan su Shi suke kira da suna (HOLOCAUSTS) ya Sanya a makarantu koyar da Dalibai Qin yahudawa. kuma doka ce ko Ruwa aka kama ka kaba bayahude kashe ka za'ayi kaida Shi, Domin haka ya karanta Tarihi a shekarun da Suka shude qasar Germany ta taba korar yahudawa acikin qasar.




Hitler ya hada Kai da Qasar ITALY da Qasar JAPAN sun qulla kawance inda Ashekarar 1939 Hitler yayi umurni ga Generals din Shi dasu kwace ikon qasar POLAND, Bayan nan Hitler ya tura gagarumar Runduna su kwace qasar FRANCE , SPAIN, PORTUGAL duka qasashen turai da basu Goya masa Baya Sai ya mamaye su da karfin soji, wannan Abu ya tayar ma da Qasar England wacce ke a gefen Germany amma Ruwan teku sun shiga tsakanin su Wanda haka yasa ita ma England din Bai mamaye ta ba. Amma sojojin Sama sunyi luguden wuta acikin biranen qasar England, lamarin Hitler ya tayar da Hankalin hatta America dukda cewa America Hankalin ta ya karkata ne ga qasar JAPAN da fadan gasar Tattalin Arziki ya rikide zuwa wuta-wuta, amma Nan take shugaban qasar England wato Prime Minister na loqacin da suke kira (WINSTON CHURCHILL) Ya aika da saqon Gaugawa ga shugaban America (FRANKLIN DELANO ROSOVELT)
Kan cewa Hitler na barazana ga hatta qasar England data rage Mai motsi a loqacin, yayi Kiran karfafa qawancen soja Domin taka ma Germany Birki, ita Kuma America yaqin ta da Dan Hakin daka raina wato JAPAN ya Sha Mata Kai amma a haka ta cije ta Aika ta rudunar sojoji qasar England Domin Tsaurara Tsaro!



Mu haɗu a rubutu na uku.

✍️ Abbas Ibrahim Zauma.

Comments

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

Dangane da Schorlarship ɗin gwamnatin jihar Kano

TARIHIN HITLER (08)