TARIHI WAYE ADOLF HITLER?

 

Adolf Hitler haifaffen Dan qasar (AUSTRIA) Mu kula akwai babanci tsakanin qasar AUSTRIA da AUSTRALIA. Qasar AUSTRIA wata qaramar qasa ce dake makwaftaka da Qasar GERMANY dake turai. An haife Adolf Hitler a shekarar "1889" Adolf Hitler tun Yana qarami ya rasa iyayen sa yayi rayuwar maraici Kuma yasha wahalar rayuwa,  Hitler mutum ne Mai baiwar Zane-zane (Arts)  Kuma mutum ne Mai son Tarihi, ya taso Kuma ya Girma acikin qasar sa ta haihuwa AUSTRIA Mai makwaftaka da GERMANY, mutun ne Mai Qin Jinin Yahudawa Kuma Yan tuhumar shugabannin Turai da Daure ma yahudawa suna juya turai da qasashen su na Gado yadda suke so! Tare da zargin shugabanni da fifita yahudawa Akan "Yan Asalin qasashen su, loqacin da wannan ra'ayin ya fara bayyana ga wannan matashin mutun Sai aka daqile yunkurin sa na shiga Aikin soja Kuma aka rufe Shi a gidan yari tsawon loqaci, Bayan fitowar sa Sai ya wallafa wani littafi Mai suna (MY STRUGGLE}  Ma'ana GWAGWARMAYA TA.

  


Daga nan Bayan rashin samun cikakkiyar dama daga Qasar sa ta AUSTRIA Sai ya yanke shawarar yaga Indigent nashi na qasar ya Koma qasar GERMANY Mai makwaftaka da AUSTRIA Wanda Hitler yayi imanin cewa qasar Germany ma qasar su ce ta Gado Domin ma kusan Harshen su daya Kuma Al'adun su daya Qasar Germany ta karbi baquncin matashi Hitler ya zama Dan qasa ya samu sabon (NATIONALITY)  Wanda yayi Hakane a shekarar 1913 ana saura shekara daya a fara Gwabza yaqin DUNIYA na farko (WWI}  nan take Hitler ya shiga Aikin soja Amma cikin Volunteer ma'ana Sojan Sakai.


✍️ Abbas Ibrahim Zauma

#Spaddaawah

Comments

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

Dangane da Schorlarship ɗin gwamnatin jihar Kano

TARIHIN HITLER (08)