Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya saka wa dokar bai wa daliban kasar na manyan makaratun da suka fito daga gidajen masu karamin karfi damar samun rancen karatu maras ruwa daga gidauniyar bayar da bashin karatu ta kasar. A watan Nuwamban shekarar da ta wuce ne majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin dokar, da ke neman kafa wata gidanauniyar za ta rika ba daliban manyan makarantun kasar bashin kudin makaranta. Sabuwar dokar dai ita ce irinta ta farko a Najeriya kuma in ji Shugaban ma’aikata na Fadar Shugaban Kasar Femi Gbajabiamila, wanda shi ne ya kawo kudurin dokar lokacin yana kakakin majalisa, za ta inganta kasar domin babu wani yaron Najeriya da za a hana wa damar samun ilmi mai zurfi saboda rashin kudi. Gabanin fito da wannan dokar dai, bankuna a kasar kan bayar da bashin kudin karatu ne ga iyayen yara ko shi ma da tsauraran sharudda da kuma takaitaccen lokacin biya. Da yawa dalibai masu rangwamen gata a kasar kan jingine karatu mai zurfi saboda rashin kudi ko kuma ...
Comments
Post a Comment