Gwamnan jihar Kano ya kai ziyara katsina
Mai girma Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf a wannan rana ta asabar 03/06/2023 ya kai wata ziyarar kulla zumunci tsakaninsa da maƙwabciyar jihar Kano (Jihar Katsina).
Yayin wannan ziyara mai girma Gwamna ya samu tarba ta musamman daga wajen gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Radda wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jihar ta Katsina tare da shugaban ma'aikata na jihar ta Katsina gami da hamshaƙin ɗan kasuwar nan Alhaji Dahiru Barau Mangal.
Salisu Yahaya Hotoro
03 06 2023.
masha Allah
ReplyDelete