FALALAR BIN IYAYE //006//


BIYAYYA GA IYAYE.

Cikin Alƙur'ani mai girma, akwai ayoyi masu kira zuwa bautar Allah shi kaɗai amma a haɗe da kyautata wa iyaye, daga cikinsu akwai inda Allah (S.W.T) Yake cewa:

"Ku bautawa Allah kada ku hada wani da Allah kuma ku kyautata ga iyaye".

Suratun: Nisa'i, Ayah: (36).

A nan Allah (S.W.T) Ya nuna mana ibada ba ta karɓuwa sai da biyayya ga iyaye, shi ya sa Manzon Allah (S.A.W) ya ce a cikin Hadisin da Amru ɗan Aljuhani ya ce:

Haƙiƙa wani mutum yazo wajen Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Ya Manzon Allah (S.A.W) na shaida haƙiƙa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma kai Manzon Allah ne. Na yi salloli biyar na ba da zakkar dukiyata, na yi Azumin watan Ramadan. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce  wanda duk ya mutu a kan wannan yana tare da Annabawa, da Siddiƙai da shahidai ranar Alƙiyamah. Haka sai Annabi ya haɗa yatsun sa biyu kuma ya ce matuƙar bai saɓa wa iyayensa ba. (Imamu Ahmad da Ɗabarani suka rawaito da dangane mai kyau).

Wannan Hadisi yana nuna mana duk biyayyar da za ka yi wa Allah (S.W.T) ba za ka sami amfaninta ba matuƙar kana saɓa wa iyayenka. Haka ma babu yadda imani zai zauna a zuciya matuƙar ana saɓa wa iyaye, kuma su iyayen fa ba lalle ne su zama Musulmi ba, sai fa in sun neme ka ne da saɓawa Allah (S.W.T) to anan ba za ka bi su ba.

Mu haɗu a rubutu na gaba!

Daga: Littafin Falalar bin iyaye da hatsarin saɓa musu, wallafar Ustaz Tijjani Bala ƙalarawi.

Rubutawa: ✍️
Muhammad Abdulrahman Rano

Comments

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

Dangane da Schorlarship ɗin gwamnatin jihar Kano

TARIHIN HITLER (08)