FALALAR BIN IYAYE //005//
YADDA WASU SUKA MAIDA ƳAN UBA (II).
A nan ya kamata in jinjina wa mata masu zumunci, su ma ba duka ba. domin zumuncin mata ba kamar maza ba, wajen ziyara, suna, biki, tare da ciyarwa. Sai fa wadda shaiɗan yayi mata huɗuba ta kauce. Ya kamata in jawo hankalin ɗan uwa wanda Allah (S.W.T) ya yi wa baiwa ta kuɗi, amma ƴaƴansa basu dashi. To ya ji tsoron Allah kadda ya maida ƴaƴansa ba komai ba, saboda kawai ya fi su abin hannu; ya riƙa wulaƙanta su.
Mai yiwuwa ma ya barsu a ƙauye, ya shigo birni. Wani ma ba ya so a same shi cikin abokansa a ce masa ga ƴan uwan babanka nan, ko na babarka sunzo. sai ya canza fuska, wai zasu kunyata shi cikin abokansa. Ya kamata duk mai hankali ya yi ƙoƙarin kyautata zumunci tsakaninsa da ƴan uwan mahaifiya tasa, da mahaifinsa. Kuma ya kula da zumuntar ƴaƴan ƴan uwansa maza da mata ya riƙa ziyartasu. yana yi musu aike a kai a kai in mabuƙata ne.
Kuma koda ba mabuƙata ba ne ya wajaba a kyautata musu koda ta hanyar wasiƙa, ko saƙon baka. Kuma yayi iya ƙoƙarinsa ya ga tarbiyar ƴan uwansa ta yi kyau, yaga ya rabasu da shaye shayen miyagun ƙwayoyi. Kar yace bashi ya haife su ba, ko kuma ba uwa ɗaya uba ɗaya suke ba. A'a ya kamata ya sowa ƴan uwansa alkairi ya kuma ƙi musu sharri, kamar yadda yake yiwa kansa. Kuma ya wajaba ka zama mutumin kirki a cikinsu.
Mu haɗu a rubutu na gaba!
Daga: Littafin Falalar bin iyaye da hatsarin saɓa musu, wallafar Ustaz Tijjani Bala ƙalarawi.
Rubutawa: ✍️
Muhammad Abdulrahman Rano
Comments
Post a Comment