FALALAR BIN IYAYE //004//

YADDA WASU SUKA MAIDA ƳAN UBA (I).

Ba ƙaramin sharri ba ne a ce iyaye su zura ido su ga ƴaƴansu maza da mata ba su jituwa, haka kawai. wai saboda ubansu ɗaya maimakon suyi zumunci na ƴan uwantaka irin wanda Allah da manzonsa suke so. sai su ɗauki wata baƙar gaba, kai kace gabar musulmi ce da kafiri a wajen yaƙi. kuma wai har sai kaji ana cewa ƴan uba ai daga Annabi Yusuf (A.S) aka samo. To, wannan ba ƙaramar ƙarya bace.

Ƙissar Annabi Yusuf (A.S) tana da hikimomi da yawa, ba labarin haɗa rigima take ba, ba kuma koyar da rigima take ba, maimakon haka tana ma ƙara haɗa zumunci, tare da ƴan uwa da soyayya da yafewa, da nemawa juna rahamar Allah, tare da girmama mahaifi da neman addu'arsa mai albarka. da kuma matso da ƴan uwa  kusa, su ma suci arziki yayin da ɗan uwansu Allah ya yi masa wata ni'ima.

Domin a yanzu an kusa, ko kuma an wayi gari ƙani baya ganin girman wansa, sai in yanada kuɗi koda kuwa uwa ɗaya uba ɗayane. balle kuma ace uba ɗayane, haka ta kai ɗan wa baya ganin girman ƙanin ubansa ko wan ubansa tana yiwuwa ma suna gari ɗaya baya gaisheshi. sai anyi mutuwa su haɗu, ko kuma wajen ɗaurin Aure, daga nan kuma sai wani lokaci. 

Mu haɗu a rubutu na gaba!

Daga: Littafin Falalar bin iyaye da hatsarin saɓa musu, wallafar Ustaz Tijjani Bala ƙalarawi.

Rubutawa: ✍️
Muhammad Abdulrahman Rano

Comments

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

Dangane da Schorlarship ɗin gwamnatin jihar Kano

TARIHIN HITLER (08)