FALALAR BIN IYAYE //003//

RASHIN TARBIYA DA RASHIN TSAWATAWA (II)

Wani uban abin kunya idan akace ana son ƴarsa da aure sai kaji yace se abinda Hajiya tace. Kuma lallai ya kamata uba ya sa ido akan karatun ƴaƴansa, biyan kuɗin makaranta. bayan ciyarwa da shayarwa da tufatarwa tare da tsawatarwa, da sa ido akan abokan ƴaƴansa ko ƙawayen ƴarsa: saboda gudun ɗaukar mummunar ɗabi'a. 

Haka ma ya zama wajibi iyaye musanman uba, su sa ido game da zuwa biki da liyafar aure da shaƙiyai kan shirya bayan ɗaurin aure. domin yanzu abun ya ƙazanta da gaske, matuƙar iyaye suka bar ƴaƴansu ba sa sa ido to duk abinda ya faru kar suyi kuka da kowa sai kansu. Hakanan kar iyaye su sa san duniya a zuciyarsu saboda kawwai sunada kyakyawar ƴa, ko kuma suna ganin su ƴan dangi ne, ko kuma me neman ƴarsu su me da shi ba komai ba saboda shi ba wane bane ba kuma ɗan wane bane.

Kai harma sai kaga yarinta ta bijirewa iyayenta saboda kawai wai sun matsa mata. haka ma yana da kyau iyaye su nisanta ƴaƴansu daga kallon fina - finai na batsa dan shima yana jawo raina magabata saboda sharrin da abin yake haifarwa. hakama kadda iyaye suyi shiru yayin da sukaga wani marar hankali shashasha, ɗan shaye -shaye, ɓarawo ko me neman mata ta baya yana son ƴarsu suyi shiru kawwai wai saboda ze basu abin duniya.

Mu haɗu a rubutu na gaba!

Daga: Littafin Falalar bin iyaye da hatsarin saɓa musu, wallafar Ustaz Tijjani Bala ƙalarawi.

Rubutawa: ✍️
Muhammad Abdulrahman Rano

Comments

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

Dangane da Schorlarship ɗin gwamnatin jihar Kano

TARIHIN HITLER (08)