FALALAR BIN IYAYE //002//

RASHIN TARBIYYA DA RASHIN TSAWATAWA. (I)

Wani lokaci ba banza ba za ka ga raini ya shiga tsakanin iyaye da ƴaƴa, ko da yake ba hujjah bace. Amma idan aka duba yadda ake aure barkatai kuma da yadda yara suke ganin iyayensu na dukan iyayensu mata, ko kuma yadda iyaye mata kan cukume rigar miji tqnq ɗura masa zagi; kai harma wani lokaci zakaga yadda salacin uba kan haifar da ƴaƴan kishiya su yi wa matar ubansu duka, ko kuma wasu iyaye maza da kan aikata wasu munanan halaye a gaban ƴaƴansu.

Wasu iyayen ƴaƴansu na sa ne da irin ɓarnar da suke shukawa, kamar ajiye matan banza a wasu wurare na musanman, ko kama musu gidaje don zaman tare ba bisa sunnar Annabi ba, ko shaye - shaye ko aikata wasu miyagun laifuka; wanda haƙiƙa yana haifar da raini tsakanin iyaye da ƴaƴa. Amma fa uwa da uba komai suke ba hujja bace a ce ƴaƴansu su raina su biyayyar su daban tsakaninsu da iyayensu, wadda Allah ya wajabta musu amma a nan ina nuna wa iyayene kada su riƙa yin abin da zai jawo raini tsakaninsu da da ƴaƴansu.

Haka ma lallai iyaye su ga cewa ƴaƴansu sun rungumi sallah a kan lokaci saboda hadisin Manzon Allah (S.A.W) inda yace; "ku hori ƴaƴanku da sallah sune shekara bakwai, ku buge su in sun kai goma, amma ba bugu mai fasa jiki ba, wato in sunƙi sallah. kuma ku raba tsakaninsu wajen kwanciya". Sau dayawa wasu iyaye ba sa son a faɗi laifin ƴaƴansu wai saboda soyayya. kuma bazasu iya yi musu faɗaba wani lokaci kuma sau dayawa ƴaƴa su yi aikin ashsha wai sai kaji uba yana cewa in ka ƙi dainawa zan gaya wa Hajiya don nasan kafi tsoranta.

Mu haɗu a rubutu na gaba!

Daga: Littafin Falalar bin iyaye da hatsarin saɓa musu, wallafar Ustaz Tijjani Bala ƙalarawi.

Rubutawa: ✍️
Muhammad Abdulrahman Rano

Comments

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

Dangane da Schorlarship ɗin gwamnatin jihar Kano

TARIHIN HITLER (08)