FALALAR BIN IYAYE //001//

GABATARWA.

Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki tsira da Amincin Allah su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta kuma cikamakin manzanni. shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W) da Alayensa da sahabbansa tare da mabiya sunnah tasa, har zuwa ranar ƙarshe.

Bayan haka jama'ar musulmi ina mai farin cikin gabatar muku da wannan littafi mai albarka, wato me suna "FALALAR BIN IYAYE DA HATSARIN SAƁA MUSU" wallafar Babban Malami Sheikh Tijjani Bala ƙalarawi wanda ni Muhammad Abdulrahman Rano ɗan ƙaramin ɗalibi nake rubutawa a kafafen sadarwa.

Malam ya cigaba da cewa: Ban fassara waɗannan hadisai ba sai bayan nayi zurfin tinani a kaina da jama'ar musulmi masu yawa, waɗanda ƴaƴansu suke kyautata musu, kuma na sadu da wasu jama'a da dama a wasu jihohin Nijeriya masu kwatanta biyayya ga iyayensu, da irin fa'idar da suke gani sakamakon biyayya. haka ma na sadu da waɗanda suka guje wa iyayensu don basu da hali, suka maida kawunansu ƴaƴan wasu masu hali, suka cigaba da bautawa wasu ƙarti bauta marar lada! babu ko godiya, ga kuma rashin albarka cikin duk abinda suka samu.

Ji da gani na irin waɗannan haɗarori da muka shiga, shi yasa na rubuta wannan littafi, ko Allah (S.W.T) ya tsame wadanda suke saɓa wa iyayensu daga halaka zuwa tsira, kuma ya amfani manya, waɗanda ko dai sun saɓawa iyayensu a baya kuma iyayen sun mutu ba su shiriya ba, ko kuma iyayen suna da rai amma babu jituwa tsakaninsu, wato basa ganin girman iyayen, da fatan za su yi ƙoƙarin kyautatawa iyayensu saboda su samu rayuwa mai albarka duniya da lahira.

Mu haɗu a rubutu na gaba!

Daga: Littafin Falalar bin iyaye da hatsarin saɓa musu, wallafar Ustaz Tijjani Bala ƙalarawi.

Rubutawa: ✍️
Muhammad Abdulrahman Rano

Comments

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

Dangane da Schorlarship ɗin gwamnatin jihar Kano

TARIHIN HITLER (08)