MUHIMMANCIN TAIMAKON MARAYU



Daga: Malam Ɗayyabu Umar Memai Rano.

Tsoron Allah shi ke bada zaman lafiya amma da yake masu imani suke temakawa marayu se aka gano zaman lafiya na nan zinƙir a temakawa marayu kamar yanda aka bayyana.

Misali kamar duk wanda yaga anyi mutuwa marayun da aka bari suna samun kulawar gaske daga al'umar Annabi (ﷺ) to bazai ji tsoron mutuwa akan gaskiya da ɗaukaka Addinin musulunci ba, bugu da ƙari bazai sace kuɗaɗen al'umma ba dan tarawa ƴaƴansa ba don yaga yadda marayu suke samun kulawa.

Kaga kenan waɗanda suke kwashe kuɗin al'umma don su tarawa ƴaƴansu zasu ragu. masu ɓoye dukiyarsu domin su taskacewa ƴaƴansu zasu ragu. wanda hakan ze kawo raguwar masu shiga wuta. 

✍️ Muhammad Abdulrahman Rano
10 Jumada Sani 1444 AH
03 January 2023 M

Comments

Popular posts from this blog

Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya

Dangane da Schorlarship ɗin gwamnatin jihar Kano

TARIHIN HITLER (08)