HADISIN YAU NA (06)
Daga: Mal. Aminu Ibrahim Daurawa.
FALALAR KARANTA SURATUL IKLAS.
Manzon Allah (ﷺ) yace: "Duk wanda ya karanta ƙulhuwallahu ƙafa goma Allah zai gina masa gida a Aljannah".
FA'IDA;
Wannan sura ta ƙunshi tsantasan tauhidi na kaɗaita Allah ta'ala da kore masa kishiya. Tana koyar da kaɗaita Allah da bauta. Tana koyar da kaɗaita Allah
acikin sunaye da siffofi da kuma kai masa buƙatu. Tana kore farko da ƙarshe da be haifa ba ba'a haifeshi ba. Tana korewa Allah ta'ala kishiya acikin hallittinsa.
Shi Kaɗaine acikin rububiyya (yin halitta da mallakar halitta) da Uluhiyya (kaɗaita shi da bauta) da Asma'i wassifati (kaɗaita shi acikin sunayansa da siffofinsa).
Muhammad Abdulranman Rano
facebook.com/muhdabdulrano
Comments
Post a Comment