HADISIN YAU NA (04).
Daga; Mal. Aminu Ibrahim Daurawa.
FALALAR ZIKIRI A KOWANNE HALI.
Daga Nana Aisha (رديلله عنه) tace: "Manzon Allah (ﷺ) yana Ambaton Allah a kowanne Hali.
Ibnul Ƙayyum yace; Manzon Allah (ﷺ) yana Ambaton Allah a dukkan yanayi har ambaton Allah ya zama kamar numfashi a gareshi, yana tsaye ko yana zaune ko yana kwance ko yana cikin tafiya ko yana kan abin hawa ko a halin tafiya ko a zaman gida a ko ina ya sauƙa zikiri yakeyi".
FA'IDA
Wannan hadisi yana koya mana mu shagala da zikiri da ambaton Allah a kowanne lokaci da kowanne hali, yafi zaman gulma da tsurku da Annamimanci da cin naman mutane da ƙage da ƙazafi wanda yayi yawa a wannan zamani.
Muhammad Abdulranman Rano
facebook.com/muhdabdulrano
linktr.ee/muhdabdulrano
Comments
Post a Comment